Tauraron Queqiao, ya tsaya ne kilomita 100 a saman wata, kamar yadda aka ba shi umarni daga cibiyar dake kula da ayyukansa dake Beijing, sannan ya sauya yankin shawaginsa.
A cewar Manajan kula da aikin tauraron, dama kalilan tauraron yake da ita na tsayawa, saboda takaitaccen makamashi da yake da shi.
A ranar Litinin da ta gabata ne aka harba tauraron, domin samar da hanyar sadarwa tsakanin doron kasa da tauraron Chang'e 4, mai binciken barin duniyar wata mai nisa.
Ana sa ran tauraron zai daidaita shawaginsa sau da dama, kafin ya isa yankin shawagi na L2 mai nisan kimanin kilomita 455,000 daga doron kasa. (Fa'iza Mustapha)