in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu nasarar harba sabon tauraron dan Adam na sadarwa
2018-05-04 10:40:13 cri

Yau Jumma'a da misalin karfe 12 da minti 6 na sanyin safiya, kasar Sin ta yi nasarar harba sabon tauraron dan Adam kirar APSTAR-6C ta hanyar amfani da rokar dakon kaya kirar Long March-3B daga cibiyar harba tauraron dan Adam na Xichang da ke kudu maso yammacin kasar.

Harba tauraron dan Adam na APSTAR-6C, shi ne na 12 da kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin ya gudanar bisa yarjejeniyoyin kasa da kasa, wato yarjejeniyar da kamfanin masana'antu na Great Wall na kasar Sin karkashin shugabancin kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin da kamfanin tauraron dan Adam na sadarwa na Asiya da tekun Pasific na Hong Kong suka daddale a watan Oktoba na shekarar 2015.

Kwalejin nazarin fasahar sararin samaniya na kasar Sin ne ya tsara fasalin wannan tauraron dan Adam na APSTAR-6C ya kuma kera shi. Tauraron dan Adam din zai daina aiki ne bayan shekaru 15. Za a kuma yi amfani da shi ne wajen aikin sadarwa da hidimomin rediyo a yankin Asiya da na tekun Pasific. Sa'an nan kuma, yayin da ake kyautata yadda tauraron dan Adam na APSTAR-6C da takwarorinsa suke ba da hidimar aikin sadarwa, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin za ta kara samun karbuwa, lamarin da zai samar da kyakkyawar makoma ga kasuwanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China