Jami'in kula da sashen tsare-tsare na ma'aikatar sufurin kasar Sin Peng Siyi ya bayyana cewa, kasarsa tana kokarin ganin ta mallaki tauraron dan-Adam dinta na BeiDuo sannan ta sanya shi cikin tsarin hukumar zirga-zirgar jiragen saman kasa da kasa da sauran tsare-tsaren sadarwa na kasa da kasa masu nasaba da hakan.
Jami'in wanda ya sanar da hakan a yau Laraba yayin wani taron manema labarai, ya ce manufar hakan ita ce, yadda tauraron dan-Adam na BeiDou na kasar Sin zai taimakawa harkokin kasa da kasa da kuma yadda za a kammala tsarin cikin tsare-tsare sadarwa na duniya.
Peng ya ce tuni hukumar zirga-zirgar jiragen ruwa ta duniya da tsarin bincike da aikin ceto na taurarin dan-Adam na duniya suka amince da tsarin na BeiDou.
Ya kuma bayyana tabbacin cewa, tsarin na BeiDou zai iya gogayya da sauran tsare-tsare taurarin dan-Adam, amma kuma da akwai sauran aiki kafin ya karade duniya baki daya.(Ibrahim)