Kasar Sin ta harba tauaroron dan Adam mai amfani naurar da za ta iya sarrafawa shi daga nesa wato Remote, da misalin karfe 3:44 na asubahin yau Talata agogon birnin Beijing, inda ta yi amfani da rokar Long March 2C wajen harba shi, daga cibiyar harba tauroron dan Adam ta Xichang dake lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar.
Tuni tauraron da aka ayyana nasarar harba shi ya fara shawagin shirin fara aiki.
A matsayinsa na kashi 3 na tauraron Yaogan-30, tauraron zai gudanar da binciken muhalli da ya shafi lantarki da maganadisu da sauran wasu gwaje-gwaje. (Fa'iza Mustapha)