in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan tsalle cikin ruwa
2018-05-11 06:45:41 cri

Wasan tsalle cikin ruwa, wane dake matsayin hanyar nishadi mai dadaden tarihi. Wata tsohuwar shaida da ta nuna yadda aka gudanar da wasan a can da, ita ce wani zanen da aka zana cikin wani kabarin da aka gina shi a Italia kimanin shekaru 2500 da suka wuce, wanda ya nuna yadda wani saurayi ya tsalle cikin ruwa daga wani dandali mai tsayi.

Duk da cewa an dade ana gudanar da wasan tsalle cikin ruwa a matsayin wani wasa na nishadi, amma ba a taba shirya wata gasar zamani bisa wasan ba sai zuwa shekarun 1880, lokacin da aka fara gudanar da gasannin wasan tsalle cikin ruwa a kasar Birtaniya. Wata hukuma mai sunan "hadaddiyar kungiyar masu wasan ninkaya ta kasar Birtaniya" ta kafa gasar fasahar tsalle cikin ruwa a shekarar 1883, daga bisani aka samu gasa mai alaka da wasan tsalle cikin ruwa da ake gudanarwa a duk shekara, har zuwa shekarar 1937 lokacin da aka dakatar da gasar.

A lokacin, ana kokarin gwada fasahar tsalle cikin ruwa daga wani dandali mai tsayi sosai, musamman ma a kasar Birtaniya. Sai dai a nasu bangaren, jama'ar Sweden da Jamus sun fi nuna sha'awa ga wasan tsalle da juya jiki a sama kafin a fada cikin ruwa. Wannan salon wasan tsalle cikin ruwa ya fara yaduwa zuwa sauran kasashe, lamarin da ya sa aka kafa wasa na "Fancy Diving", wato wasan tsalle tare da yin wasu motsi na musamman, irinsu lankwasa da jujjuya jiki, kafin a sauka cikin ruwa. Zuwa shekarar 1904, an fara gudanar da gasar wasan tsalle cikin ruwa daga wani dandali mai tsayi a wasannin Olympics. Sa'an nan a wajen wasannin Olympics da suka gudana a birnin London a shekarar 1908, an fara gudanar da gasar wasan "Fancy Diving". (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China