in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan kwallon damben kasar Kenya ya sha alwashi yin galaba a gasar Commonwealth
2018-03-15 14:43:59 cri
Dadadden dan wasan damben kasar Kenya Nick Abaka, ya lashi takobin samun lambar zinare ta wasan damben Commonwealth da za'a dambata tsakanin ranakun 4 zuwa 15 ga watan Aprilu.

Abaka, mai shekaru 38 da haihuwa, zai sake bayyana a wasan damben a karo na biyu, amma ya kwana da masaniyar cewa a wannan karon yanayin fafatawar da za'a yi zata kasance mai zafi ce.

Sai dai kuma, dama ya jima yana baiwa kansa cikakken horo gami da kyakkyawar fatar da yake da ita na cewa zai kasance mai matukar karfi kuma zai yi kokarin rage nauyinsa domin kaucewa fuskantar abin takaici makamancin wanda ya fuskanta a zagayen kusa da na kusan karshe na gasar wasan damben da aka gudanar a Glasgow, na kasar Scotland a shekarar 2014.

Yace, "zan bayyana a karo na biyu a wasannin Commonwealth, tun bayan lokacin dana wakilci Kenya a shekarar 2014 a wasan damben da aka fafata a Glasgow, na kasar Scotland."

"Yanayin wasa a wannan mataki yana bukatar karfi, sai dai ya danganta da irin shirin da na yi wanda shine ke bani kwarin gwiwa, a wannan karon zan lashe lambar yabon," inji Abaka ya fada a ranar Lahadi daga Nakuru.

Ga mutumin da ya tsunduma cikin wasannin dambe tun a shekarun 1990 da suka gabata, ya yi amanna yana da cikakkiyar kwarewar da zai iya yin galaba kuma har ya kai kansa matsayin lashe lambar yabon.

"A matsayina na cikakken soja, ina da ragowar harsashe guda a tare da ni. Glasgow ya kasance mabudin ido. Na kai matsayin wasan kusa da na kusan karshe. A wannan karon ina son na matsa zuwa mataki na sama kuma zan kai ga mataki na karshe," injishi.

Bugu da kari, mafarkin dan wasan dambe Mohammed Ali na samun lambar zinare a wasan Commonwealth ya gamu da cikas sakamakon bacewar sunansa cikin jerin sunayen 'yan wasan dambe su 7 na kasar Kenya wadan da zasu halarci wasan damben.

Shugaban tawagar 'yan wasan kasar Kenya Barnaba Korir ya bayyana cewa, dama babu sunan Ali cikin 'yan wasan da aka zaba amma a maimakon hakan an sanya sunan Brian Agina ne.

Shugaban kungiyar 'yan wasan damben kasar Kenya John Kameta yace Ali bashi da koshin lafiya kuma bai samu halartar bada horo ba a makonni ukun da suka gabata tun bayan da ya dawo daga wasan damben da aka gudanar a Delhi na kasar Indiya a watan jiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China