in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan Tsalle
2018-04-01 11:16:38 cri

Wasan Tsalle, wato Long Jump a Turance. Wasan yana daya daga cikin wasannin da ake gudanar da su cikin filayen wasa ko kuma kan hanyoyin tsere. Wanda yake bukatar dan wasa ya samu karfin jiki da gudu cikin sauri, ta yadda zai iya tsalle har ma ya kai wani wuri mai nisa. Bayan ya yi tsalle ya kuma dira a kasa, za a auna nisan dake tsakanin wurin da ya yi tsalle da inda ya dira. Kuma a cikin gasar wasan tsalle, dan wasan da nisan tsallensa ya fi na sauran 'yan wasa shi ne ya yi nasara ke nan.

A nan kasar Sin, makarantu na daukar wannan wasa a matsayin wata dabarar inganta karfin jiki da lafiyar dalibai. Don haka, idan ka samu damar zuwa makarantun firamare, ko kuma na sakandare, za ka ga yaran kasar Sin na halartar wasan tsalle a filin wasa, musamman ma a lokacin darasi na motsa jiki. Har ma akan sanya jarrabawar musamman a fannin darasi na motsa jiki, inda ake kayyade nisan da za a yi tsalle a matsayin wani ma'aunin da zai tabbatar da lafiyar jikin dalibai. Idan wani dalibi ya yi tsalle kuma nisan tsallensa bai kai matsayin da ake bukata ba, to, za a bukace shi ya kara motsa jiki, sa'an nan ya sake shiga jarrabawa don cimma matsayin da ake bukata.

Ban da wannan kuma, a kusan dukkan manyan gasannin wasan motsa jiki da ake gudanar da su a nan kasar Sin, a kan samu gasar wasan tsalle, tun da wasan ya kasance wani wasa mai muhimmanci cikin wasannin da ake gudanar da su a filayen wasa ko kuma kan hanyar gudu. Wannan shi ne takaitaccen bayani game da yadda ake gudanar da wasan tsalle a nan kasar Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China