in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Darasi na motsa jiki
2018-04-24 15:19:01 cri

Ban da amfani ga lafiyar jiki, ayyukan da ake yi cikin darasin PE da kuma sauran wasannin motsa jiki da dalibai suke shiga a makaranta, su ma suna da amfani sosai a fannin kara hazakarsu. Har ma akwai shaidu da suka nuna cewa, daliban da suke yawan halartar wasannin motsa jiki, sun fi samun damar samun sakamako mai kyau a fannin karatu, idan an kwatanta da daliban da ba su son motsa jiki. Kana dalilin da ya sa haka shi ne domin shiga wasannin motsa jiki a kai a kai zai taimakawa mutane mai da hankali kan littattafan da suke karantawa, da kuma rike abubuwan dake cikinsu.

Kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha sun taba gudanar da wasu gwaje-gwaje kan wasu gungun mutane daban daban, ga misali, tsoffin mutane, da wadanda suke zama a cikin gidan kurkuku, gami da kananan yara. Sa'an nan sakamakon gwaje-gwajen ya nuna cewa, tsoffin mutanen da ba su son motsa jiki, kwakwalwarsu tana tsufa cikin sauri, har ma saurin tsufarta ya fi na jikin mutum. Kana 'yan kaso da suke da al'adar yin tafiya sun fi saukin mai da hankali kan wani aiki, ko kuma tunawa da wasu abubuwa, idan an kwatanta da mutanen da suke son tsayawa gida.

A fannin daliban makarantar firamare kuma, yaran da su kan yi tafiya zuwa makaranta, sun fi wadanda suke shiga motocin bus domin zuwa makaranta, wajen damar samun maki mai kyau a jarrabawa.

Dalilin da ya sa motsa jiki ke da wannan amfani na kara hazakar mutum, a cewar masu nazarin kimiyya da fasaha, shi ne domin ta hanyar motsa jiki, karin jini zai shiga cikin kwakwalwarmu, abin da zai taimaka mata aiki. Kana, wasu sinadaran da jikinmu ya samar da su yayin da yake motsi su ma suna da amfani ga kyautata yanayin kwakwalwarmu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China