Cikin wata sanarwar da ya fitar, kakakin ma'aikatar Heather Nauert, ya ce rangadin da Rex Tillerson zai yi a karon farko, zai kai shi Chadi da Djibouti da Habasha da Kenya da kuma Nijeriya.
Yayin rangadin, Sakataren zai gana da shugabannin kasashen da kuma shugabancin Tarayyar Afrika dake da mazauni a birnin Addis Ababa na Habasha, a yunkurin Amurka na kulla kawance da gwamnatoci da al'ummar Afrika.
Takamaimai dai, Rex Tillerson na da shirin tattauna hanyoyin da Amurka da nahiyar Afrika za su yi aiki tare, wajen yaki da ta'addanci da wanzar da tsaro da zaman lafiya da inganta shugabanci na gari da kuma lalubo damarmakin ciniki da zuba jari da bangarorin biyu za su ci gajiya. (Fa'iza Mustapha)