Kasar Sin ta zuba makudan kudade wajen bunkasa lantarki a yankunan karkarar Xinjiang
![]( /mmsource/images/2018/02/27/e82a998442664a4fbf5e5d2e2d7abfb0.jpg)
Hukumar raya ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin ta ware kudi kimanin yuan biliyan 2.65 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 420 domin bunkasa lantarki a yankunan karkara na Xinjiang Uygur mai cin gashin kai cikin wannan shekarar.
Shirin bunkasa lantarkin ya amfanawa manoma da makiyaya sama da miliyan 4 a yankin na Xinjiang a cikin shekaru 5 da suka gabata. Masana'antun dake sarrafa 'ya'yan itatuwa da masu sana'o'in hannu da kuma masu kiwon dabbobi duka sun ci moriyar wannan shirin a yankin. (Ahmad Fagam)