Kasar Sin za ta bunkasa amfani da fasahar jirage marasa matuka a fannin harkokin sufurinta don kara ingantashi, da samun kyakkyawan yanayi a fannin.
Li Xiaopeng, ministan sufuri na kasar Sin ya tabbatar da hakan a ranar Laraba, ya ce a halin yanzu an fara shirye shiryen tsara yin amfani da fasahar ta jiragen marasa matuka don kafa wani ingantaccen tsari.
Li ya ce, ya yi amanna amfani da fasahar zai haifar da kyakkyawar makoma a sha'anin sufurin kasar ta Sin kasancewar tuni an riga an fara amfani da fasahar a wasu bangarorin da suka hada da bangaren jiragen kasa na zamani.
Li ya ce, ma'aikatar ta fara aikin kafa cibiyar gudanar da bincike a wannan fanni.(Ahmad Fagam)