Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, na shirin samar da kasuwar bai daya ta hada hadar sufurin jiragen sama, matakin da zai kasance na farko a jerin ajandojin nahiyar na samar da ci gaba nan da shekarar 2063.
Za a kaddamar da kudurin wanda aka yiwa lakabi da SAATM ne a birnin Addis Ababan kasar Habasha, a ranar 28 ga watan nan yayin taron kungiyar da yanzu haka ke gudana.
Shirin SAATM zai bude karin damammaki na bunkasa hada hadar cinikayya, da damar zuba jari tsakanin kasashe daban daban, musamman a fannonin samar da kayayyaki da ba da hidima, ciki hadda yawon bude ido, matakin da zai samar da karin guraben ayyukan yi na kai tsaye kimanin 300,000 da wasu karin ayyukan dake bijirowa miliyan 2.
Da yake karin haske game da hakan, kwamishinan kungiyar mai lura da harkokin makamashi da samar da ababen more rayuwa Amani Abou-Zeid, ya ce kaddamar da SAATM zai hade sassan tattalin arzikin nahiyar, ya kuma fadada ci gaban ta baki daya.
Yanzu haka dai sashen sufurin jiragen sama na Afirka na tallafar al'ummun nahiyar kimanin miliyan 8 ta fuskar samar da guraben ayyukan yi, yayin da ake sa ran SAATM zai fadada wadannan damammaki.
Kaza lika ana sa ran shirin zai share fage ga sauran muhimman ajandojin ci gaban Afirka 12 na nan da shekarar 2063, ciki hadda kaddamar da fasfo na bai daya ga al'ummar nahiyar, da tsarin cinikayya cikin 'yanci na bai daya ga 'yan nahiyar ko CFTA a takaice.
Wata sanarwar da aka fitar a yayin taron na AU dake gudana ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, kasashen Afirka 23 cikin 55 ne suka amince da shiga tsarin na SAATM, yayin da 44 kuma suka sanya hannu kan yarjejeniyar Yamoussoukro, wadda ta tanaji kariya ga kasuwannin nahiyar.
An bude taron kungiyar ta AU karo na 30 ne a ranar Litinin a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha.(Saminu)