in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jigilar kayaki ya samu habaka cikin watan Mayu
2017-06-28 10:12:11 cri
Ma'aikatar Sufuri ta kasar Sin ta ce an samu karuwar ayyukan jigilar kayayyaki cikin watan Mayu, wanda alama ce da ke nuna hada-hadar harkokin tattalin arziki.

Rahoton da ma'aikatar ta fitar jiya ya ce hanyoyin sufuri da suka hada da na jiragen kasa da motoci da na ruwa sun yi jigilar jimilar ton biliyan 4.06 na kayayyaki a watan Mayu, wanda ya karu da kasha 9.9 a kan na bara, inda ya dara na watan Afrilu da kashi 0.2.

A cewar ma'aikatar, jigilar kayayyaki cikin watanni 5 na farkon shekarar nan, ya karu da kashi 9.5 a kan na bara, inda ya kai ton biliyan 17.62. (Fa'iza Mutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China