Ministan ma'aikatar sufuri ta kasar Sin Li Xiaopeng, ya ce kasar na fatan kara yawan jari da take zubawa a fannin bunkasa harkokin sufuri a shekarar 2018 dake tafe.
Li Xiaopeng ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yana mai cewa, a wannan shekara ta 2017, ana sa ran jarin kai tsaye a fannin ginin layukan dogo da manyan titunan mota zai kai darajar kudin Sin Yuan biliyan 800, da kuma kusan Yuan Tiriliyan 1.65 a shekarar dake tafe.
Ministan ya kara da cewa, a shekarar dake tafe za a gina manyan tituna masu tsawon kilomita 5,000 tare da fara amfani da su a shekarar. Kaza lika za a gyara tituna masu tsawon kilomita 200,000 a sassan yankunan karkara, da karin hanyoyin sufurin ruwa masu tsawon sama da kilomita 600.
Bugu da kari, kasar ta Sin za ta ci gaba da mai da hankali ga gina hanyoyin mota a yankuna mafiya fama da talauci, domin cimma burin nan na hade yankunan da manyan hanyoyin kasar nan da shekarar 2020.
Ya ce, a shekaru 3 masu zuwa, fannin sufuri zai taka muhimmiyar rawa wajen yaki da talauci, da bunkasa ci gaban yankunan kasar cikin kyakkyawan yanayi ba kuma tare da gurbata muhalli ba.(Saminu)