A jiya Talata ne, a yayin babban taron kiwon lafiya na kasa da kasa karo na 70 da aka yi a birnin Geneva, shugabar hukumar kula da harkokin kiwon lafiya da shirin kayyade iyali ta kasar Sin Li Bin ta taya Tedros Adhanom Ghebreyesus murnar lashe zaben shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO.
Ms. Li ta bayyana imanin cewa, za a cimma burin samun dauwamammen ci gaba ta fuskar ayyukan kiwon lafiya nan da shekarar 2030, bisa hadin gwiwar dake tsakanin hukumar WHO karkashin jagorancin Ghebreyesus da sauran kasashen duniya. (Maryam)