Majalisar ta ce ta yi matukar kaduwa game da samun labarin kalaman da Trump ya furta inda ya tozarta al'ummar Afrika da mutanen dake da tushen Afrika.
Majalisar ta ce wadannan kalamai sun yi matukar muni, kuma ba daidai ba ne shugaba irin na Amurka ya aikata haka, majalisar ta kara da cewa, a nahiyar Afrika ana matukar girmama dattijai kuma ana girmama kalaman da dattijai ke furtawa musamman irin kalaman da suka yi amfani da su wajen bayyana matsayarsu. Shugaban Amurka dattijo ne kuma wajibi ne a ko da yaushe ya rika mu'amala irin ta dattijai, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce ana girmama mutanen duniya ne bisa matsayinsu da kuma irin yadda suke mutunta kalaman dattaku da suke furtawa. Yin amfani da kalamai wajen nuna wariyar launin fata wani mataki ne da zai kara ruruta wutar rikici a duniya wanda ake samun yawaitar hakan a wasu sassan duniya.
Sanarwar ta ce sun bukaci shugaban na Amurka da ya gaggauta janye kalaman nasa, kuma ya nemi afuwar dukkan al'ummar Afrika da mutanen dake da tushen Afrika a duk fadin duniya. (Ahmad Fagam)