Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar Afirka AU Moussa Faki Mahama ya amince da tura wata tawagar masu sanya ido a zaben shugabancin kasar Liberia da ake gudanarwa a yau, bayan da kotun kolin kasar ta jinkirta gudanarsa a kwanakin baya, sakamakon zargin aikata a zagayen farko na zaben.
Shugaban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yau Talata, ta bayyana cewa, tawagar wadda ta isa kasar ta Liberia tun a ranar 23 ga wannan wata, za ta kasance a kasar har zuwa ranar 31 ga wata.
'Yan takara biyu ne dai ke fafatawa a zaben, wato George Weah na jami'yyar CDC da kuma mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai na jam'iyyar UP mai mulkin kasar.(Ibrahim Yaya)