A wata sanarwa da ya fitar, Mahamat ya bukaci mambobin kasashen na AU, da al'ummomin raya tattalin arziki na shiyyar (RECs), da sassan kungiyar ta AU, da kungiyoyin fararen hula, da jama'ar kasashen na Afrika, da dukkan masu ruwa da tsaki a nahiyar da su hada gwiwa don yin aiki tare a shekarar ta 2018 da ma bayanta, wajen dakile ayyukan rashawa wanda ke jefa rayuwar al'ummar kasashen cikin mawuyacin hali, musamman talakawa da mutane marasa galihu a cikin al'umma.
Mahamat ya nanata muhimmancin daukar karin matakai wajen shawo kan matsalolin.
Tun bayan da aka ayyana shekarar 2018 a matsayin shekarar yaki da rashawa a nahiyar Afrika, jami'ai da kuma sassan dake tafiyar da al'amurran kungiyar ta AU, ke cigaba da daura damara ta yakar ayyukan da suka jibinci rashawa don samar da zaman lafiya da ceto nahiyar ta Afrika. (Ahmad Fagam)