Shugaban hukumar zartaswar AU, Moussa Faki Mahamat, ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen makonnin cewa, ya gamsu da yadda aka kulla yarjejeniyar dakatar da tashin hankalin da tsagaita bude wutar tsakanin sassan biyu, wanda aka daddale a Kinkala.
Shugaban ya mika sakon fatan alheri ga dukkan bangarorin, inda yace wannan wani muhimmin mataki ne a kokarin da ake wajen lalibo bakin zaren warware rikicin da ya addabi jamhuriyar Congo.
Sai dai ya gargadi bangarorin da abin ya shafa dasu mutunta yarjejeniyar da aka kulla.
Yace aiwatar da daftarin dake kunshe cikin yarjejniyar zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kuma samar da kyakkyawan yanayin cigaban rayuwar al'ummar Kongo da inganta sha'anin mulkin demokaradiyya a kasar.