Ma'aikatar shari'a ta kasar Sin ta bayyana cewa, a halin yanzu akwai mutane 700,000 da aka yanke wa hukuncin yi wa al'umma aiki a matsayin gyara halinka .
Shugaban sashen gudanarwa na shirin gyara halinka Jiang Aidong shi ne ya bayyana hakan a jiya Litinin 18 ga wata, yana mai cewa, tun lokacin da aka bullo da wannan shiri a matsayin gwaji a shekarar 2013, zuwa wannan lokaci kimanin mutane miliyan 3.5 ne suka gudanar da aikin gyara halinka a cikin al'umma, inda aka samu kaso 0.2 cikin 100 na mutanen da suka sake komawa ruwa.
Jiang ya yi kira da a yi amfani da kyawawan al'adun Sinawa wajen ilimantar da masu aikata laifi tare da samar musu kayayyakin inganta rayuwa.
Jami'in ya kara da cewa, akwai bukatar a kara yin kirkire-kirkire domin inganta abubuwan dake kunshe cikin tsarin da yadda ake gudanar da irin ayyukan gyara halinka a cikin al'umma.(Ibrahim)