Yau Jumma'a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kasar Sin ta amince da bayanin da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, haka kuma, duk da canje-canjen da ake samu a duniya, dadaddiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ba za ta canja ba.
Kwanan baya ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, al'ummomin kasar Rasha sun amince da raya dangantakar dake tsakanin kasar Rasha da kasar Sin, a saboda haka, duk yadda sakamakon babban zaben shugabancin kasar ya kasance, kasarsa za ta ci gaba da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasar Sin.