Bugu da kari, kasar ta Sin ta gabatar da wasu manyan shirye-shiryen guda 8 a fannonin al'adu da musaya tsakanin jama'a, da kasashen da suka hada da Rasha da Amurka da Burtaniya da Faransa, Sauran sun hada da Jamus da Indonesiya da kuma Afirka ta kudu.
Haka kuma ya zuwa karshen shekarar 2016, ma'aikatar Ilimi ta kasar ta Sin ta amince da hukumomi da shirye-shiryen koyar da Ilimi kimanin 2,500 da aka bude tsakanin Sin da kasashen waje.
Ma'aikatar ta kara da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata kasar Sin ta kulla hadin gwiwa a fannin Ilimi da musaya da kassashe da yankuna 188. (Ibrahim)