A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake jaddada manufar gwamnatin tsakiyar kasar, game da martaba manufar nan ta "kasa daya tsarin mulki iri biyu" a yankunan Hong Kong da Macao.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manyan jami'an yankunan biyu na musamman a nan birnin Beijing.
Yayin ganawarsa da gwamnar yankin Hong Kong Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, shugaba Xi ya yaba da irin manufofi da matakai da gwamnatin Lam ta dauka wajen bunkasa tattalin arziki, inganta rayuwa da yanayin zamantakewar al'ummmar yankin tun lokacin da ta kama aiki a watan Yulin wannan shekara.
Shugaba Xi ya ce, gwamnatin tsakiyar kasar ta yaba da aikin Lam da na sabuwar gwamnatin yankin Hong Kong. Yana mai cewa an rubuta manufar nan ta "kasa daya, tsarin mulki iri biyu" da yayata akidar sake hada kan kasa cikin rahoton babban taron wakilan JKS karo na 19 da aka kammala a kwanakin baya, a matsayin muhimmiyar manufar gina tsarin Kwaminisanci mai sigar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki.
Ya ce, wannan ya nuna yadda gwamnatin tsakiya ke daukar batun yankunan Hong Kong da Macao da muhimmancin gaske. Haka kuma ya nuna yadda ta dade tana martaba wannan manufa ta "kasa daya mai bin tsarin mulki iri biyu", manufar da babu mai goge ta.(Ibrahim)