Shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta Kudu ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, duk da cewa kasarsa ta rungumi akidar sasantawa da gina kasa tun a shekarar 1994, amma har yanzu kan al'ummar kasar a rabe yake a fannoni al'adu da bambancin launin fata.
Shugaba Zuma wanda ya bayyana hakan cikin wani sako da ya aikewa 'yan kasar albarkacin ranar sasantawa na kasa da ta fado a yau Asabar 16 ga watan Disamba, ya ce, yana da muhimmanci a gare mu baki daya mu kara hada kai mu yi aiki tare domin ci gaban kasarmu da wadanda muke zaune a cikinta.
Zuma ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga 'yan kasar, da su yi aiki tare a matsayinsu na 'yan kasa domin yayyata akidar sasantawa, zaman lafiya da hadin kan al'umma.
Taken bikin ranar ta bana dai shi ne " Shekarar Olibo Tambo gwarzon yaki da wariyar launin fata na kasar. Sasantawa ta hanyar farfado da tattalin arziki da jin dadin jama'a. (Ibrahim)