Ko da a cikin shekarun baya bayan nan, kasashen Afirka sun dukufa wajen raya harkokin intanet, amma ana fuskantar wasu matsaloli wajen aiwatar da ayyukan da abin ya shafa, kamar yawan jahilai a kasashen Afirka, da karancin gina ababen more rayuwa da kuma tsadar kudin yin amfani da intanet da dai sauransu. (Maryam)