A gun taron, karamin jakadan Sin dake birnin Johannesburg Ruan Ping ya bayyana cewa, ana raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a shekarun baya baya nan, kasar Afirka ta Kudu ta riga ta zama kasa mafi girma ta abokiyar ciniki ta kasar Sin, kana ta zama muhimmin wurin zuba jari da yawon shakatawa na kasar Sin.
Shugaban reshen Johannesburg na bankin kasar Sin Cheng Jun, ya bayyana cewa, tare da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", da hadin gwiwar Sin da Afirka ta Kudu, babu shakka za a shiga sabon matsayi na hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya a nan gaba. (Zainab)