Hukumar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu da abin ya shafa ta bayyana cewa, ana fatan yin amfani da wannan hanya don sassauta tsaron masu yawon shakatawa daga kasashen waje da suka zo kasar Afirka ta Kudu, da jin dadin yawon shakatawa, da kawar da damuwa ta fuskar fashi da jin rauni. Ma'aikatar harkokin yawon shakatawa ta kasar za ta tura maza da yawan shekarunsu ya kai 18 zuwa 35 zuwa mashahuran wuraren yawon shakatawa don tabbatar da tsaro da samar da hidima a fannin yawon shakatawa a wuraren. (Zainab)