Mahalarta dandalin tattalin arzikin duniya kan Afrika na shekarar 2015 (WEF Afrika) sun jaddada a ranar Alhamis cewa, ci gaban matasa na kasancewa kamar wani gishikin ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afrika.
A yayin bude dandalin a birnin Cape Town, shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya yi kira ga kasashen Afrika da su bai wa matasa babban matsayi domin su taka rawarsu a fagen ci gaban Afrika.
Ya kuma jaddada muhimmancin ganin kasashen Afrika sun samar da tsare tsare domin shigar da matasa cikin harkokin tattalin arziki, da kuma ba su damar yin jagoranci.
A cewar wasu hasashe, nan da shekarar 2040, matasa a Afrika za su wakiltar kashi 50 cikin 100 na matasan duniya, in ji babban shugaban WEF mista Klaus Schwab dake jagorantar taron budewa. A nahiyar Afrika ya kamata a kafa ayyukan yi miliyan 18 a ko wace shekara domin kwashe matasan da ke shiga cikin kasuwar kwadago.
Mataimakin shugaban kasar Ghana, Kwesi Amissah-Arthur, a yayin da yake amsa tambayoyi a yayin zaman muhawara, ya jaddada cewa, ci gaban Afrika na dogaro sosai da wayewar kan matasa, musammun ma kan ilimi da karfafa kwarewa, wato yana da muhimmanci ga matasa da su koyon ilmi da kuma samun aikin yi, in ji mista Amissah-Arthur. (Maman Ada)