in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in AU ya bukaci a dauki matakan samar da 'yancin zirga-zirga a cikin nahiyar Afrika
2017-10-17 12:54:41 cri

Daraktan kula da harkokin siyasa na hukumar tarayyar Afrika Khabele Matlosa, ya ce akwai bukatar gaggauta samar da muhimman manufofi da tsarin shari'a da za su saukakawa jama'a zirga-zirga a nahiyar Afrika.

Khabele Matlosa, wanda ya bayyana yayin taron AU kan tsare-tsaren kaura da 'yan ci rani da 'yan gudun hijira da ya gudana jiya a Kigali, babban birnin Rwanda, ya ce tsare-tsaren za su saukaka amfani da fasfo na Afrika da zirga-zirga cikin kasashen nahiyar ba tare da visa ba, da samar da yankin cinikayya maras shinge, domin inganta hadin kan nahiyar.

Taron ya samu mahalarta sama da 200 daga fadin nahiyar, ciki har da ministoci da masana a bangarorin da suka shafi kaura da ci rani da gudun hijira bisa tilas.

Taron na da nufin tattaunawa da duba yiyuwar daukar matakan yarjejeniyar da ta shafi zirga-zirgar jama'a ba tare da shinge ba da hakkin zama a wata kasa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China