Jami'ai daga kasashen Afirka na tattaunawa a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka AU da ke Addis Ababa kan hanyoyin magance matsalolin da ke kawo tarnaki ga jin dadin jama'a a nahiyar Afirka.
Taron wanda sashen kula da jin dadin jama'a na hukumar kungiyar AU ya shirya, zai kuma duba batutuwan da suka shafi kwadago da batun samar da ayyukan yi.
Bugu da kari, taron wanda zai gudana daga ranar 20 zuwa 24 ga watan nan na Afrilu, zai kuma duba hanyoyin magance kalubalen da mata ke fuskanta, kana ya tattauna hanyoyin da suka dace a dauka kan yadda za a inganta matsayin mata a bangaren samun ayyukan yi, da kuma yadda za a kare matsayinsu.
Har ila taron zai duba shirin nan na shekaru biyar na farko da majalisar kungiyar AU ta kirkiro wadda aka kaddamar a watan Janairun shekara ta 2015 kan batun samar da ayyukan yi, kawar da talauci da kuma samun bunkasuwa.
A cewar kungiyar AU, batun tasirin da cutar Ebola ta yi a kasashen da cutar ta fi kamari a nahiyar na daga cikin abubuwan da za a tattauna ckin ajandar taron.(Ibrahim)