Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya nanata muhimmancin zuba jari ga sha'anin ci gaban matasan nahiyar Afrika kuma a magance matsalar nuna banbancin jinsi don ci gaban nahiyar.
Ya yi wannan kiran ne jiya a lokacin bude taron makon Afrika, wanda ya kasance wani muhimmin biki a MDD.
Guterres ya ce, Afrika ita ce nahiyar da ta fi samun yawan karuwar matasa a duniya. Don haka abu mafi muhimmanci shi ne a zuba jari mai yawan gaske a fannin ilmi, musamman ilmin kimiyya da fasaha, domin hakan zai baiwa matasan damar shiga a dama da su wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar. Ya kara da cewa, ana bukatar a samu mutane masu kwarewa don amfanarwa rayuwar al'ummar dake rayuwa a wannan zamani har ma da al'ummomi masu zuwa a nan gaba.
Ya jaddada muhimmancin tallafawa mata da 'yan mata. Kana ya bukaci yin amfani da kirkire-kirkire da samar da kudade a matsayin hanyoyin da za su samar da ci gaba. Mista Guterres ya ce, abin da ya fi dacewa shi ne, kamata ya yi kasashen Afrika su sauya fasalin tsarin kudaden haraji a tsakaninsu, kuma su hada kai da kasa da kasa domin yakar hanyoyin da kudaden harajinsu ke zurarewa da kuma yaki da halasta kudin haram da zambar kudade wanda ke haddasa matukar hasara ga tattalin arzikin nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)