Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Hu Haitao ya bukaci kasa da kasa su ba da gudunmowa ga Afrika damin ciyar da tattalin arziki da yanayin zamantakewar al'ummar nahiyar gaba.
Wu Haitao, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a lokacin bude babban taro na makon Afrika a helkwatar MDD, inda ya bukaci kasashen duniya su kara azama wajen samarwa Afrika ci gaba, ta yadda nahiyar za ta iya dogaro da kanta.
Ya ce, ya kamata kasa da kasa su bunkasa harkokin noma irin na zamani a Afrika, da bunkasa harkokin masana'antu, da samar da makamashi, da inganta fannin sufuri, ta yadda Afrikar za ta iya tsayawa da kafafunta. Kana ya bukaci kasa da kasa su mutunta 'yancin ikon kasashen na Afrika, musamman wajen tallafa musu wajen tsara shirye-shiryen da za su tabbatar da ci gaban kasashen nasu.
Wu ya kuma bukaci kasashen duniyar su inganta tsarin harkokin kasa da kasa wanda zai tabbatar da ci gaban Afrika. Ya kamata kasa da kasa su kara daukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika da sauran bangarorin duniya. Ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su yi amfani da salon tuntubar juna, da ba da gudunmowa, da samar da moriya domin kara samar da wakilci da yin magana da muryar kasashe masu tasowa wajen tabbatar da ci gabn harkokin tattalin arzikinsu. Mista Wu ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su aiwatar da manufofin da za su tabbatar da ci gaban kasashe masu tasowa, daga ciki akwai kasashen nahiyar Afrika, don samun ci gaban tattalin arziki da kyautatuwar rayuwar al'umma.(Ahmad Fagam)