Rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai na kasar Amurka, sun bayyana a jiya Lahadi cewa, sakamakon sallamar da wata kotu ta yiwa wani dan sanda da aka zarge da hallaka wani bakar fata, zanga-zanga ta barke tare da tashin hankali a daren ranar Asabar 16 ga watan nan a birnin Saint Louis na jihar Missouri, lamarin da ya haifar da fasa shaguna fiye da 20, da lalata motocin 'yan sanda 5, da kuma jikkatar 'yan sanda 9. Sakamakon haka, an kama masu zanga-zanga fiye da 30.
An ce dai rashin isassun shaidu ne suka sanya tsohon dan sanda Jason Stockley kubuta daga laifin da ake zargin sa da aikatawa a ranar 15 ga wata, na kashe wani matashi dan asalin Afirka a shekarar 2011. (Kande Gao)