An samar da wannan bayanai ne tun lokacin da kwamitin kula da harkokin kasuwan na gwamnatin tarayya yayi wata ganawa a watan Yuli inda ya nuna cewa guraben samar da ayyukan yi na kasar suna cigaba da samun tagomashi, kuma harkokin tattalin arzikin kasar yana samun matsakaicin cigaba a cikin shekarar bana. Amurkar ta sanar da hakan ne bayan kammala wani taron yini biyu kan sha'anin kudin kasar a ranar Laraba.
Mahukunta kasar ta Amurka suna fatar cigaban tattalin arzikin kasar zai cigaba da bunkasa cikin matsakaicin yanayi a nan gaba.
A bisa hasashen karuwar tattalin arzikin da gwamnatin kasar tayi wanda aka fitar da rahoton a ranar Laraba, jami'an gwamnatin Amurkar sun yi hasashe samun karuwar tattalin arzikin kasar da kashi 2.4 cikin 100 a wannan shekara, sama da hasashen kashi 2.2 cikin 100 da aka yi a watan Yuni.(Ahmad Fagam)