Rex Tillerson ya ce suna kan nazarin batun domin yana da muhimmanci gaya, la'akari da illar da ya yi wa wasu mutane, inda ya ce sun mai da wasu daga cikinsu gida.
Daga bisani hukumomin Amurkan sun tabbatar da cewa, Amurkawa a kalla 21 ne suka yi fama da alamomin cuta.
Babu cikakken bayani da aka fitar game da cutar, sai dai kafafen yada labarai sun ruwaito cewa wasu daga cikin Amurkawan sun gamu da lalurar ji, yayin da a kalla mutum guda gamu da matsala a kwakwalwa.
A watan Yulin 2015 ne Amurka da Cuba suka farfado da huldar diflomasiyya a tsakaninsu, bayan ya shafe sama da shekaru 50 cikin mawuyacin hali. (Fa'iza Mustapha)