Bisa wannan kuduri, gamayyar kasa da kasa za su rage yawan man fetur da suke samarwa Koriya ta Arewa, sannan za a hana kasar fitar da kayan saka zuwa ketare tare da kuma haramtawa mutanen kasar da ke kasashen waje tura kudi zuwa kasar.
Da wadannan matakai, ana neman hanawa kasar damar gudanar da shirinta na samar da makaman nukiliya da masu linzami.
Bayan kammala jefa kuri'a don zartas da kudurin, Liu Jieyi, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD, ya ce kasar Sin na kalubalantar Koriya ta Arewa don ta lura da burin gamayyar kasa da kasa na ganin ta dakatar da aikin samar da makaman kare dangi, tare da maido da aikin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya.(Bello Wang)