Shugaba Xi ya ce Sin na cikakkiyar biyayya ga ka'idojin MDD, wadanda suka shafi hana yaduwar makaman Nukiliya, tare da burin wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin, baya ga batun warware takaddamar da ake yi kan hakan, tsakanin sassan masu ruwa da tsaki ta hanyar tattaunawa.
Kaza lika shugaban na Sin, ya ce hanya daya tilo ta warware takaddamar ita ce maida hankali kan matakan sulhu, yana mai cewa hada tattaunawa da matakai masu ma'ana, za su haifar da sakamakon da ake bukata.
A nasa bangare kuwa, Mr. Trump cewa ya yi kasar sa ta damu matuka, game da halin da ake ciki a zirin Koriya, tana kuma dora muhimmancin gaske, game da rawar da Sin ka iya takawa, wajen kawo karshen yanayin dar dar da ake ciki. Don haka shugaba Trump ya sha alwashin ci gaba da tattauanwa da tsagin Sin, a wani mataki na ganin an kai ga fidda jaki daga duma. (Saminu)