Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar jiya, Antonio Guterres ya jadadda kira ga shugabancin Koriya ta arewa da ya dakatar da yin gwaji tare da biyayya ga dokokin kasa da kasa karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD.
Ya ce wannan matakin sake sabawa dokokin kasa da kasa ne da kuma tarnaki ga yunkurin kasashen duniya na kawar da makamai. Inda ya bayyana gwajin a matsayin wanda ke barazana ga tsaron yankin.
Kakakin ya ce sakatare janar din zai ci gaba da tuntubar dukkan bangarorin da abun ya shafa.
A jiya Lahadi ne Jamhuriyar Demokradiyyar Al'ummar Koriya, DPRK ta yi gwajin makami mai linzami mafi karfi, tana mai ikirarin kirkirar bom mafi karfi mai sinadarin hydrogen da za a iya makalawa jikin linzamin da za a iya harbawa daga wata nahiya zuwa wata. (Fa'iza Mustapha)