Kwamitin ya ba da sanarwar ne a jiya Jumma'a, yayin wani taron manema labarai da ya kira.
Rahotanni na cewa, makasudin shirya babban taron shi ne, aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na MDD da ake son cimmawa zuwa shekarar 2030 da tsara wani sabon shirin musamman bisa yarjejeniya game da shirin kandagarki da magance kwararar Hamada, domin cimma burin yaki da kwararar hamada, da kuma neman taimakon kudade daga bangarorin da abin ya shafa.
An yi hasashen cewa, taron zai samu halartar wakilai kimanin 1,400, wadanda za su hada da, wakilan gwamnatoci 196 da suka kulla yarjejeniyar cikin hadin gwiwa, da kuma wasu wakilai na kungiyoyin kasa da kasa da na kungiyoyi masu zaman kansu.
A halin yanzu, an kusa kammala ayyukan shirya babban taron mai taken "kandagarki da magance kwararar Hamada cikin hadin gwiwa, domin ba da tallafi ga dukkanin bil Adama". (Maryam)