Jiya Talata da dare ne, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwar shugaba, inda ya yi kakkausar soka da harba makamai masu linzami da kasar Koriya ta Arewa ta yi a kwanan baya. Sanarwa ta kuma bukaci Koriya ta Arewa da ta martaba kudurorin MDD ta kuma gaggauta daina harba makamai masu linzami.
Sanarwar ta kara da cewa, abin da Koriya ta Arewa ta yi yana kawo barazana ga yankin da ma kasashe mambobin MDD. A saboda haka, sanarwar ta bukaci Koriya ta Arewa da ta hanzarta yin watsi da wannan mataki na rashin hankali, da ma duk wasu makaman nukiliya da shirinta na kokarin mallakar makaman nukiliya har abada, kana ta dakatar da duk wasu sabbin gwaje-gwajen nukiliya, ta kuma dakatar da daukar matakan tsokana, ta kuma yi watsi da ragowar makaman kare kangi da ta mallaka. (Tasallah Yuan)