Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harba makami mai linzami mai nisan zango dake da karfin kaiwa wata nahiya, da Jamhuriyar Demokuradiyyar al'ummar Korea ta yi.
Wata sanarwa da mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ya fitar jiya, ta ruwaito Antonio Guterres na cewa, harba makamin sake take dokokin kwamitin sulhu na majalisar ne.
Sanarwar ta ce dole ne shugabancin kasar ta yi cikkaken biyayya ga dokokin kasa da kasa tare da yin aiki da al'ummomin kasashen waje domin warware matsalolin da suka shafi zirin Korea.
Sakatare Janar din ya jadadda yin kira ga shugabancin Jamhuriyar Demokuradiyyar al'ummar Korea, ta mai da martini ga bukatar Jamhuriyar Korea, ta sake bude hanyoyin sadarwa musammam tsakanin rundunonin soji domin rage rashin fahimta da fargaba. (Fa'iza Mustapha)