Matakin zai haramtawa DRPK samun damar fitar da ma'adananta na kwal, karfe, tama da karafa, darma da abincin ruwa. Kudurin zai kuma haramtawa kasashen duniya kara yawan ma'aikatan kwadagon na DPRK dake ayyuka a kasashen waje da kuma haramta sabbin zuba hannayen jari a kasar.
Kuduri mai lamba 2371, ya samu amincewar dukkan wakilan mambobin kwamitin tsaron MDDr a ranar Asabar, wanda ya karfafa matakan aza takunkumin kan DPRK ne don mayar da martani kan gwajin makaman nukilyar da ta gudanar a ranar 3 da kuma 28 ga watan Yuli.
Daukar wannan mataki, ta bayyana a fili cewa, kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da saba ka'idojin da DPRK ke yi kuma ana bukatar kasar da ta dakatar da shirinta na makaman nukiliyar baki daya.(Ahmad Fagam)