Wang Yi ya ce, da sanyin safiyar yau Lahadi, kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani sabon kudiri wanda ya shafi batun nukiliyar zirin Koriya. A matsayinta na kasa mai wakilicin dindindin a kwamitin sulhun MDD, Sin tana taka rawar a-zo-a-gani wajen warware matsalar nukiliyar Koriya ta Arewa.
Wang ya ce, wannan sabon kudiri na kunshe da manyan fannoni biyu. Na farko, kwamitin sulhun ya maida martani game da harba makaman nukiliya da Koriya ta Arewa ta rika yi, ta yadda za'a dauki matakai na hana duk wani yunkuri na Koriya ta Arewar na raya makaman nukiliyarta. Na biyu shi ne, a yi kira da a farfado da shawarwari tsakanin bangarori shida, da warware batun nukiliyar zirin Koriya ta hanyar lumana da siyasa, domin kaucewa tabarbarewar halin da ake ciki a yankin.(Murtala Zhang)