Wani wurin dake da tazarar kilomita kimanin 200 zuwa arewacin birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, akwai wani filin dashe na itatuwa da ake kiransa "Sai-Han-Ba". Sai dai idan ka tafi wurin wasu shekaru 55 da suka wuce, za ka ga tamkar hamada ce, abin da za a iya gani rairayi ne kawai. Amma wadanne mutane ne suka taimaka wajen gyara muhallin wurin?