Babban jami'in tsare tsare na shirin cimma moriya daga albarkatun kasar na MDD Dirk Wagener, ya ce wajibi ne a samar da dokoki da tsare tsare, wadanda za su baiwa nahiyar Afirka damar kaucewa gurbacewar yanayin muhalli, tare da rungumar matakai da za su inganta amfani da makamashi mai tsafta.
Mr. Wagener, wanda ke tsokaci yayin taron kaddamar da shirin kyautata yanayin kare muhalli a kasar Kenya ko SAG a takaice, ya ce kamata ya yi gwamnatoci su yi hadin gwiwa da sassa masu zaman kan su, wajen magance kalubalen dake addabar nahiyar a wannan fanni, kamar dai sauran nahoyiyoyi takwarorin ta.
A cewar jami'in, tsare tsaren da ake fatan nahiyar za ta aiwatar, su ne za su taimaka wajen karfafa ci gaban harkoki masu nasaba da amfani da makamashi mai tsafta, tare da wanzar da dorewar manufofi masu alaka, karkashin wani tsari da aka yiwa lakabi da SCP.
Bugu da kari Mr. Wagener ya ce, tun kaddamar da SAG karon farko a kasashen nahiyar Afirka, shirin ya samar wa sassan masu ruwa da tsaki 34 kudade, da tallafin kwararru, da darajar su ta kai dalar Amurka miliyan 11.5. Kasashen da suka ci gajiyar hakan kuwa sun hada da Burkina Faso, da Ghana, da Kenya, da Mauritius, da Afirka ta kudu da kuma kasar Uganda.(Saminu)