in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tona lokacin tashi da saukar jirgin saman Barack Obama a kasar Kenya
2015-07-24 09:59:32 cri
Wasu kafofin watsa labaru na kasar Amurka sun bayyana cewa sabanin tsarin boye lokacin tashi da saukar jirgin saman musamman da shugaba Barack Obama ke amfani da shi, a wannan karo an tona lokacin tashi da saukar jirgin, a daidai gabar da Obaman ke shirin kai ziyarar aiki kasar Kenya. Hakan dai ya haifar da damuwa game da shirin tsaro a yayin ziyarar ta shugaba Obama a kasar Kenya.

Bisa labarin da gidan talabijin na CNN ya bayar, an ce wani babban jami'in kamfanin jiragen saman kasar Kenya, ya bayyana lokacin rufe filayen jiragen sama da abin ya shafa ta sakon E-mail da ya aika wa abokan aikinsa, inda ya yi bayanin cewa wannan lokaci ya yi daidai da lokacin sauka da tashin jirgin sama na musammam na shugaba Obama.

Bisa ka'idojin tsaro na fadar shugaban kasar Amurka wato White House, kafin jirgin sama na musamman da shugaban kasar ke amfani da shi ya tashi, a kan rufe filayen jiragen sama da hanyoyin sama dake kewayen filin na dan lokaci, har zuwa lokacin da ayarin motocin shugaban kasar ya bar filayen jiragen saman. Ba kuma za a bayyana lokacin tashi da saukar jirgin saman na shugaban Amurka ba.

Ya zuwa yanzu dai kamfanin jiragen saman kasar Kenya bai yi karin haske game da wannan batu ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China