Cikin wasu sanarwoyi mabanbanta, Amurka da MDD sun ce ba kadai kan jami'an wanzar da zaman lafiya na AMISOM a kai wa harin na yankin Lower Shabelle ba, har ma da al'ummar da suke kokarin karewa.
Wakilin musamman na Sakatare-Janare na MDD Micheal Keating ya fada cikin sanarwar cewa, suna jinjinawa dakarun AMISOM da suka sadaukar da kansu wajen wanzar da zaman lafiya don samar da kyakkyawar makoma ga Somalia.
Har ila yau, ya ce yana kara jaddada goyon bayansu ga al'umma da gwamnatin Uganda, yayin da suke jimamin rashin 'yan kasarsu, inda kuma ya yi wa wadanda suka raunana yayin harin, fatan samun sauki.
Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka dake Somalia ta fitar kuwa ta ce, Amurka na kara nanata aniyarta ta goyon bayan shirin AMISOM wanda ke aiki da gwamnatin Somalia don samar da kasa mai cike da tsaro da zaman lafiya da kuma ci gaba. (Fa'iza Mustapha)