Za a gudanar da wadannan matakai ne a kasashe 8 ciki har da Masar, Iran, Jordan da sauransu, kuma manufar wadannan matakai da ake fatan dauka shi ne taimakawa wadannan kasashe wajen cimma burin yin amfani da albarkatun ruwa da aka tsara a ajendar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekatar 2030.
Wani jami'in MDD ya bayyana cewa, za a kara yawan albarkatun ruwa da ake yi amfani da shi ne don taimakawa kasashen dake yankin kewayen gabashin gabar tekun Mediterranean da arewacin Afirka, a wani makani na yaki da talauci, da tabbatar da tsaron abinci, da rage yawan marasa lafiya sakamakon rashin abinci da kuma inganta aikin samar da abinci. (Zainab)