A rahoton da ya gabatar jiya, Sakatare Janar din ya ce an fara aiwatar da shirin, amma lokaci na tafiya, inda ya ce rahoto ya nuna cewa, yadda ake aiwatar da shirin a wasu yankunan na tafiya a hankali sosai, kasa da yadda ake bukata domin cimma muradun a shekarar 2030.
Bisa bayanan baya-bayan nan, rahoton shekarar-shekara na shirin na nuna baki dayan kokarin da ake na aiwatar da shirin kawo yanzu, inda yake bayyana yankunan da ake samun ci gaba da kuma wadanda ke bukatar aka kara daukar matakai domin tabbatar da babu wanda aka bari a baya.
A cewar Wu Hangbo mataimakin Sakatare Janar kan harkokin da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa, karfafawa masu rauni da inganta ci gaban kowa da ko ina, na da mutukar muhimmanci wajen kawo karshen fatara. (Fa'iza Mustapha)