An zabi Adhanom ne, a lokacin babban taron hukumar lafiyar ta duniya WHO karo na 70 a Geneva, zai maye gurbin Margaret Chan, wadda take rike da mukamin tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2007.
Adhanom ya rike mukamin ministan harkokin wajen Habasha tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016, da kuma ministan lafiya tsakanin 2005 zuwa 2012
Ya taba rike hukumar kula da asusun yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta duniya AIDS, da shirin yaki da cutar tarin TB da shirin yaki da cutar Malariya, kuma ya jagoranci shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai.
A ranar 1 ga watan Yuli ne Adhanom zai kama aikin jagorancin hukumar na tsawon shekaru 5. (Ahmad Fagam)